Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 1:9kusan 629 K.H.

    Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka.

  2. Irmiya 1:10kusan 629 K.H.

    Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.”

  3. Irmiya 1:11kusan 629 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.”

  4. Irmiya 1:12kusan 629 K.H.

    Ubangiji ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.”

  5. Irmiya 1:13kusan 629 K.H.

    Maganar Ubangiji ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?” Na amsa na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, tana juyewa daga arewa.”

  6. Irmiya 1:14kusan 629 K.H.

    Ubangiji ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar.

  7. Irmiya 1:15kusan 629 K.H.

    Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji. “Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu a mashigin ƙofofin Urushalima; za su zo su kewaye dukan katangarta su kewaye dukan garuruwan Yahuda.

  8. Irmiya 1:16kusan 629 K.H.

    Zan furta hukunci a kan mutanena saboda muguntarsu na yashe ni, suna ƙona turare ga waɗansu alloli suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi.

  9. Irmiya 1:17kusan 629 K.H.

    “Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu.

  10. Irmiya 1:18kusan 629 K.H.

    Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta.

  11. Irmiya 1:19kusan 629 K.H.

    Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji.

  12. Irmiya 2:1kusan 629 K.H.

    Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  13. Irmiya 2:2kusan 629 K.H.

    “Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa, “ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki, yadda kamar amarya kika ƙaunace ni kika kuma bi ni cikin hamada, cikin ƙasar da ba a yi shuka ba.

  14. Irmiya 2:3kusan 629 K.H.

    Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji.

  15. Irmiya 2:4kusan 629 K.H.

    Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila.

  16. Irmiya 2:5kusan 629 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu.

  17. Irmiya 2:6kusan 629 K.H.

    Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji, wanda ya fitar da su daga Masar ya bishe su cikin jeji cikin hamada da kwazazzabai ƙasa mai fări da kuma duhu, ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’

  18. Irmiya 2:7kusan 629 K.H.

    Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama.

  19. Irmiya 2:8kusan 629 K.H.

    Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza.

  20. Irmiya 2:9kusan 629 K.H.

    “Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku.

  21. Irmiya 2:10kusan 629 K.H.

    Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim ku gani, ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau; ku ga ko an taɓa yin wani abu haka.

  22. Irmiya 2:11kusan 629 K.H.

    Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza.

  23. Irmiya 2:12kusan 629 K.H.

    Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji.

  24. Irmiya 2:13kusan 629 K.H.

    “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu. Sun rabu da ni, ni da nake maɓulɓular ruwan rai, sun kuma haƙa tankunan ruwansu, tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.

  25. Irmiya 2:14kusan 629 K.H.

    Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa? Me ya sa ya zama ganima?