Tsallake zuwa abun ciki

Egypt

561 verses · 4 known names

An kuma san shi da: Egyptian, Egyptians, Egyptian's

30.1000, 31.3300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Egypt

Tace bisa littafi
  1. Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.

  2. Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”

  3. Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.

  4. Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar.

  5. Bayan ya nemi shawara, sai sarki ya yi siffofin ’yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutane, “Kun daɗe kuna haurawa zuwa can Urushalima. Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar.”

  6. A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi.

  7. gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!”

  8. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.

  9. Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada

  10. Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu.

  11. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.

  12. Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?

  13. domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”

  14. Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo.

  15. Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.

  16. Ganin haka sai dukan mutane, babba da ƙarami, tare da shugabannin sojoji, suka tashi suka gudu zuwa ƙasar Masar, gama suna tsoron mutanen Babilon.

  17. Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim.

  18. Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?

  19. Aka shigo da dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye ’yan kasuwan fada suka saye su daga Kuye.

  20. Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.

  21. Babu wani abu a cikin akwatin alkawarin sai alluna biyu da Musa ya sa a cikinsa a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.

  22. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.

  23. Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”

  24. Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar.

  25. An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe.