Tsallake zuwa abun ciki

Rachel

45 ayoyi · 5 'yan gida

An kuma san shi da: Rahel

Ayoyin da suka ambaci Rachel

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Laban ya tafi don askin tumakinsa, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.

  2. Amma in ka sami wani wanda yake da gumakanka, ba zai rayu ba. Kai da kanka ka duba a gaban danginmu, ko akwai wani abin da yake naka a nan tare da ni; in ka gani, ka ɗauka.” Yaƙub dai bai san cewa Rahila ta sace gumakan ba.

  3. Saboda haka Laban ya shiga tentin Yaƙub, ya shiga tentin Liyatu da kuma tentuna matan nan biyu bayi, amma bai sami kome ba. Bayan ya fita daga tentin Liyatu, sai ya shiga tentin Rahila.

  4. Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba.

  5. Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba ’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima.

  6. Ya sa matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu a gaba, Liyatu da ’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya.

  7. Biye da su, Liyatu da ’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna.

  8. Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.

  9. Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).

  10. Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.

  11. ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin.

  12. ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali.

  13. ’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.

  14. Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.

  15. Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.

  16. Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).

  17. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

  18. Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’

  19. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.”

  20. “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.”