Tsallake zuwa abun ciki

Pharaoh

138 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Pharaoh

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna sarkin Masar, domin yă bi Isra’ilawa waɗanda suke tafiya ba tsoro.

  2. Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  3. Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji.

  4. Zan taurare zukatan Masarawa su shiga don su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.

  5. Masarawa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.”

  6. Masarawa suka bi su da dukan dawakan Fir’auna, da kekunan yaƙi, da mahayan, suka bi su cikin teku.

  7. Ruwan ya komo ya rufe keken yaƙin da mahayan, dukan sojojin Fir’aunan da suka bi bayan Isra’ilawa cikin teku, ba ko ɗaya da ya tsira.

  8. Karusan Fir’auna da sojojinsa ya jefa cikin teku. Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.

  9. Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

  10. ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.”

  11. Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.

  12. “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa.

  13. Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi.

  14. A idanunmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa.

  15. Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.

  16. Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar.

  17. alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;

  18. Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu, Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa.

  19. wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa.

  20. Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?

  21. Me ya sa kun taurare kanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka yi? Da ya ba su matsanancin wahala, ba su bar Isra’ilawa suka tafi hanyarsu ba?

  22. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

  23. A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.

  24. Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.

  25. ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna.