Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa.

  2. Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama.

  3. Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.

  4. Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.

  5. “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.

  6. Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.

  7. Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”

  8. Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.

  9. Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne?

  10. Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.

  11. Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa,

  12. suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”

  13. Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.

  14. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.

  15. Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran?

  16. Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

  17. Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba.

  18. Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.

  19. Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.

  20. Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.

  21. “Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum.

  22. “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.

  23. Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.

  24. Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”

  25. Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa.