Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi.

  2. Duk abin da ya fita daga bakinku, sai ku lura ku cika shi, kamar yadda kuka yarda da kanku, kuka yi alkawarin ga Ubangiji Allahnku da bakinku.

  3. to, kada mijinta na farko, wanda ya sake ta yă sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Wannan zai zama abin ƙyama a gaban Ubangiji. Kada ku kawo zunubi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.

  4. Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Miriyam a hanya, bayan kun fito Masar.

  5. Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku.

  6. Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.

  7. Ku tuna dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuwa ya fisshe daga can. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan.

  8. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.

  9. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  10. Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.

  11. Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.

  12. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutu daga dukan abokan gābanku kewaye da ku, a ƙasar da yake ba ku ku mallaka a matsayin gādo, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta!

  13. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta,

  14. sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa,

  15. ku faɗa wa firist da yake aiki a lokacin, “Na sakankance yau ga Ubangiji Allahnka, cewa na zo ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninmu.”

  16. Firist ɗin zai karɓi kwandon daga hannuwanku yă sa shi a ƙasa a gaban bagaden Ubangiji Allahnku.

  17. Sa’an nan za ku furta a gaban Ubangiji Allahnku cewa, “Mahaifina mutumin Aram ne mai yawo, ya gangara zuwa Masar da mutane kaɗan, ya zauna a can, ya kuma zama babban al’umma, mai iko da kuma mai yawa.

  18. Sai muka yi kuka ga Ubangiji Allahn kakanninmu, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya kuma azabar da muke sha, da wahalar da muke sha, da danniyar da suke yin mana.

  19. Sai Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi da kuma iko, da razana mai girma da kuma alamu banmamaki da al’ajabai.

  20. Ya kawo mu wannan wuri, ya kuma ba mu wannan ƙasa, ƙasa mai zub da madara da kuma zuma;

  21. yanzu kuwa na kawo ’ya’yan fari na gonar da kai, ya Ubangiji ka ba ni.” Sai ku sa kwandon a gaban Ubangiji Allahnku, sa’an nan ku rusuna a gabansa.

  22. Ku da Lawiyawa da baƙin da suke a cikinku, za ku yi murna cikin dukan abubuwa masu kyau da Ubangiji Allahnku ya ba ku tare da gidanku.

  23. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.

  24. Ban ci wani daga cikin tsattsarkan rabo yayinda nake makoki, ko in cire wani rabo mai tsarki yayinda nake marar tsarki, ko in miƙa wani sashensa ga matattu ba. Na yi biyayya ga Ubangiji Allahna, na aikata kome da ka umarce ni.

  25. Ka duba ƙasa daga sama, mazauninka mai tsarki, ka albarkace mutanenka Isra’ila da kuma ƙasar da ka ba mu kamar yadda ka yi wa kakanninmu alkawari da rantsuwa, ƙasa mai zub da madara da zuma.”