God
Ayoyin da suka ambaci God
Ku yi haka don kada a zub da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, don kada ku kuma zama masu laifin zub da jini.
Kada ka gusar da dutsen nuna shaidar iyakar maƙwabcinka wanda kakanni suka sa, a gādon da ka samu a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka mallaka.
dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.
Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku.
Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi.
Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku.
Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.
Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku.
In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.
In aka sami an kashe mutum kwance a fili, a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, ba a kuma san wanda ya kashe shi ba,
Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci.
Karɓi wannan kafara saboda mutanenka Isra’ila, wanda ka fansar, ya Ubangiji, kada kuma ka ɗaura wa mutanenka alhakin jinin mutumin nan marar laifi.” Za a kuwa yi kafarar zub da jinin da aka yi.
Ta haka za ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga cikinku, da yake kun yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, sai Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannuwanku kuka kuma kama su a matsayin bayi,
kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.
Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.
Duk wanda aka daƙe, ko yanke gabansa, ba zai shiga taron jama’ar Ubangiji ba.
Duk wanda aka haifa ta wurin cikin shege, har tsara ta goma, zuriyarsa ba za su shiga taron jama’ar Ubangiji ba, har zuwa tsara ta goma.
Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma.
Amma Ubangiji Allahnku bai saurari Bala’am ba, sai ya mai da la’anar ta koma albarka gare ku, domin Ubangiji Allahnku yana ƙaunarku.
’Ya’yan da aka haifa musu na tsara ta uku za su iya shiga taron jama’ar Ubangiji.
Gama Ubangiji Allahnku yana zagawa a cikin sansaninku don yă tsare ku, yă kuma bashe abokan gābanku gare ku. Dole sansaninku yă kasance da tsarki, saboda kada yă ga wani abu marar kyau a cikinku, har yă juya daga gare ku.
Kada ku kawo kuɗin a cikin gida Ubangiji Allahnku da aka samu ta wurin karuwanci wanda mace ko namiji ya yi don biyan wani alkawari, domin Ubangiji Allahnku yana ƙyamar su duka.
Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.