Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

  2. To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku.

  3. Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”

  4. Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

  5. ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

  6. Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

  7. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau.

  8. Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.

  9. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.

  10. Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.

  11. Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.

  12. To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.

  13. Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;

  14. alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;

  15. ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.

  16. Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,

  17. ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.

  18. Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.

  19. domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.

  20. Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.

  21. Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

  22. don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.

  23. Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.

  24. saboda kwanakinku da kwanakin ’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.

  25. In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam,