Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar.

  2. Kun ga da idanunku, manyan gwaje-gwaje, alamu masu banmamaki da al’ajabai, hannu mai ƙarfi da kuma mai ikon da Ubangiji Allahnku ya fitar da ku. Ubangiji Allahnku zai yi haka ga dukan mutanen da yanzu kuke tsoro.

  3. Ban da haka ma, Ubangiji Allahnku zai aika da rina a cikinsu, har sai sun hallaka sauran mutanen da suka ragu, waɗanda suka ɓuya daga gare ku.

  4. Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana.

  5. Da kaɗan da kaɗan Ubangiji Allahnku zai kore waɗannan al’ummai a gabanku. Ba a bari ku hallaka su duka gaba ɗaya ba, in ba haka namun jeji za su yaɗu kewaye da ku.

  6. Amma Ubangiji Allahnku zai ba da su gare ku, yana jefa su cikin rikicewa mai girma, har sai an hallaka su.

  7. Zai ba da sarakunsu a hannunku, za ku kuwa shafe sunayensu daga duniya. Babu wani da zai yi tsayayya da ku, za ku hallaka su.

  8. Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

  9. Ku hankali, ku bi kowane umarnin da nake ba ku a yau, saboda ku rayu, ku ƙaru, ku kuma shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku.

  10. Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu.

  11. Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.

  12. Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.

  13. Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.

  14. Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;

  15. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku.

  16. Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.

  17. to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.

  18. Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya.

  19. Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.

  20. In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku.

  21. Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba.

  22. Amma ku zauna da sani a yau, cewa Ubangiji Allahnku, shi ne wanda ya ƙetare ya sha gabanku kamar wuta mai cinyewa. Zai hallaka su, zai rinjaye su a gabanku. Za ku kore su, ku kuma hallaka su nan da nan, yadda Ubangiji ya yi muku alkawari.

  23. Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku.

  24. Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.

  25. Ku gane wannan, cewa ba domin adalcinku ba ne ya sa Ubangiji Allahnku yana ba ku wannan ƙasa mai kyau, ku mallaki, gama ku mutane masu taurinkai ne.