Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Firist zai ɗauki ɗan rago na hadaya don laifi tare da moɗa na mai, ya kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa.

  2. da yatsarsa na dama zai yayyafa man daga tafinsa sau bakwai a gaban Ubangiji.

  3. Sauran man da yake cikin tafinsa firist ɗin zai zuba a kan wannan da za a tsabtaccen don a yi kafara dominsa a gaban Ubangiji.

  4. ɗaya kamar hadaya don zunubi ɗayan kuma kamar hadaya ta ƙonawa, tare da hadaya ta gari. Ta haka firist zai yi kafara a gaban Ubangiji a madadin wanda za a tsabtacce.”

  5. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  6. “Sa’ad da kuka shiga ƙasar Kan’ana, wadda nake ba ku kamar gādonku, na kuma sa yaɗuwa cutar fatar jiki a riga a cikin gida a wannan ƙasa,

  7. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  8. A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist.

  9. Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.

  10. Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.

  11. Ubangiji ya yi magana da Musa bayan mutuwar ’ya’yan Haruna biyu maza waɗanda suka mutu sa’ad da suka kusaci Ubangiji.

  12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.

  13. Sa’an nan zai ɗauki bunsurai biyu yă miƙa su a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.

  14. Haruna zai jefa ƙuri’a don awaki biyun ɗin, ƙuri’a ɗaya domin Ubangiji, ɗayan kuma don azazel

  15. Haruna zai kawo akuyar da ƙuri’a ta fāɗi a kai wa Ubangiji yă miƙa ta na hadaya don zunubi.

  16. Amma za a miƙa akuyar da aka zaɓa ta wurin ƙuri’a a matsayi ta azazel da rai a gaban Ubangiji don a yi amfani da ita don kafara ta wurin korinta zuwa cikin jeji kamar azazel.

  17. Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagade a gaban Ubangiji, yă kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshin da aka niƙa yă kai su bayan labule.

  18. Zai sa turaren a wuta a gaban Ubangiji, hayaƙin turaren kuwa zai rufe murfin kafarar a bisa Akwatin Alkawari, don kada yă mutu.

  19. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade.

  20. gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku.

  21. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  22. Ubangiji ya ce wa Musa,

  23. “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.

  24. a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.

  25. Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.