Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa.

  2. waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji.

  3. Ubangiji ya ce wa Musa,

  4. Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada.

  5. Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”

  6. Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

  7. Sa’an nan ya kawo ’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi.

  8. Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  9. Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  10. Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama.

  11. Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.

  12. Sa’an nan Musa ya karɓe su daga hannuwansu ya ƙone a bagade a bisa hadaya ta ƙonawa a matsayin hadaya ta naɗi, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  13. Ya kuma ɗauki ƙirjin; rabon Musa na ɗan ragon naɗi, ya kaɗa shi a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  14. Sai Musa ya ce wa Haruna da ’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa, ‘Haruna da ’ya’yansa maza za su ci shi.’

  15. Abin da aka yi a yau umarni ne daga Ubangiji don yin kafara saboda ku.

  16. Dole ku kasance a ƙofar Tentin Sujada dare da rana har kwana bakwai, ku kuma yi abin da Ubangiji yake bukata, don kada ku mutu; gama abin da aka umarce ni ke nan.”

  17. Saboda haka Haruna da ’ya’yansa maza suka yi kome da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

  18. Ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki ɗan maraƙi domin hadayarka don zunubi da kuma ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, dukan biyu su kasance marar lahani, ka miƙa su a gaban Ubangiji.

  19. da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’ ”

  20. Suka ɗauki abubuwan da Musa ya umarta zuwa gaban Tentin Sujada, sai dukan jama’a suka zo kusa suka tsaya a gaban Ubangiji.

  21. Sa’an nan Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarce ku ku yi, domin ɗaukakar Ubangiji za tă bayyana gare ku.”

  22. Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

  23. A kan bagaden, ya ƙone kitsen, ƙodojin, da abin da ya rufe hanta, daga hadaya don zunubi, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  24. Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta.

  25. Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane.