God
Ayoyin da suka ambaci God
Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon. Sela
Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah.
Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.
Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela
Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa? Me ya sa kake ɓoye kanka a lokutan wahala?
Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.
Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.
Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.
Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”
Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah. Kada ka manta da marasa ƙarfi.
Don me mugun mutum zai ƙi Allah? Don me yakan ce wa kansa, “Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”?
Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu
Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum; ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar da ba za a gane ba.
Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.
Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda. A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.
Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.
Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.
A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu.
Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,
“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”