Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.

  2. Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya.

  3. Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.

  4. Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.

  5. In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.

  6. Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.

  7. Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

  8. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.

  9. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

  10. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

  11. wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?

  12. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

  13. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

  14. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.

  16. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.

  17. Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.

  18. Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.

  19. Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin.

  20. Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.

  21. Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.

  22. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.

  23. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  24. Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.

  25. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.