Tsallake zuwa abun ciki

Karin Magana24

Kada ka yi kishin mugaye

1
Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
2
gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.

Hikima tana ginawa da tabbatarwa

3
Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
4
ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.
5
Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
6
don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.

Wawancin mugunta da kasala

7
Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
8
Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.
9
Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
10
In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!

Ka ceci waɗanda ake jan su zuwa mutuwa

11
Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
12
In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?

Daɗin hikima da ladanta

13
Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
14
Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.

Juriyar masu adalci

15
Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama;
16
gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye.

Kada ka yi farin ciki da fāɗuwar maƙiyinka

17
Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,
18
in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.
19
Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye,
20
gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu.

Ka ji tsoron Allah ka girmama sarki

21
Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,
22
gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?

Wasu karin magana na masu hikima

23
Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
24
Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
25
Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu.
26
Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna.
27
Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka.
28
Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
29
Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”

Abin da aka lura da shi a gonar mai kasala

30
Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
31
ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
32
Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
33
Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
34
sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options