Ƙidaya 33:1-49
1
Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.
2
Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.
3
Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,
4
waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.
5
Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.
6
Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.
7
Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.
8
Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.
9
Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.
10
Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.
11
Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.
12
Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.
13
Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.
14
Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.
15
Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.
16
Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.
17
Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.
18
Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.
19
Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.
20
Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.
21
Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.
22
Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.
23
Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.
24
Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.
25
Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.
26
Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.
27
Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.
28
Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.
29
Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.
30
Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.
31
Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.
32
Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.
33
Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.
34
Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.
35
Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.
36
Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.
37
Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.
38
Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.
39
Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
40
Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.
41
Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.
42
Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.
43
Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.
44
Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.
45
Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.
46
Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.
47
Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.
48
Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.
49
A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.
Settings