Skip to content
Ƙidaya 33:3-15

Ƙidaya 33:3-15

3
Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa,
4
waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.
5
Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.
6
Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.
7
Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.
8
Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.
9
Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.
10
Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.
11
Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.
12
Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.
13
Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.
14
Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.
15
Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options