Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Widows: Allowed to share in our blessings

6 ayoyi · 56 fannoni

Ayoyi game da Allowed to share in our blessings

  1. saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.

  2. Ku kuma yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawan cikin biranenku, har ma da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikinku.

  3. Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.

  4. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.

  5. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

  6. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.