Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Union With Christ: Foundation and building

7 ayoyi · 41 fannoni

Ayoyi game da Foundation and building

  1. Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini.

  2. Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.

  3. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin.

  4. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.

  5. Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi

  6. ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi.

  7. Gama a cikin Nassi an ce, “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona, zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja, wanda kuma ya dogara gare shi ba zai taɓa kunyata ba.”