Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Truth of God

40 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.

  2. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

  3. yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.”

  4. Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu.

  5. Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci,

  6. Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

  7. Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne, dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne. Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya, shi mai adalci ne, nagari ne kuma.

  8. Bari Ubangiji yă nuna muku ƙaunarsa da amincinsa, ni kuma zan nuna muku irin wannan alherin saboda kun yi haka.

  9. Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.

  10. don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.

  11. Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.

  12. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  13. Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.

  14. Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.

  15. Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi.

  16. Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.

  17. Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari.

  18. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.

  19. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.

  20. Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

  21. Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.

  22. Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?

  23. za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.

  24. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

  25. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.