Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ammonites: Victories of Joab over

12 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Victories of Joab over

  1. Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.

  2. Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara.

  3. Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa.

  4. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa.

  5. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa.

  6. Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.”

  7. Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa.

  8. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.

  9. Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin.

  10. Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta.

  11. Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.”

  12. Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi.