Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ammonites: Punishment for oppressive cruelty

8 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Punishment for oppressive cruelty

  1. Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?

  2. Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji.

  3. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.

  4. Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku, taƙama da kwarurukanku masu amfani? Ya ke diya marar aminci, kin dogara a wadatarki kika kuma ce, ‘Wa zai iya fāɗa mini?’

  5. Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira.

  6. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.

  7. Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

  8. Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.