Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Steadfastness: Principle of-Illustrated
Ayoyi game da Principle of-Illustrated
“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.
Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.