Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shepherds: (Searching out straying sheep,) of Christ seeking the lost

7 ayoyi · 24 fannoni

Ayoyi game da (Searching out straying sheep,) of Christ seeking the lost

  1. Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.

  2. Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.”

  3. Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce,

  4. “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba?

  5. In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna,

  6. ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’

  7. Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.