Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Scribe: King's secretary

19 ayoyi · 8 fannoni

Ayoyi game da King's secretary

  1. Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.

  2. Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,

  3. masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.

  4. Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.

  5. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.

  6. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,

  7. “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

  8. Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,

  9. wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin.

  10. Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”

  11. Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.

  12. Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”

  13. Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.

  14. Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa.

  15. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,

  16. “Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”

  17. Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

  18. Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.

  19. Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu.