Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Scribe: Conspire against Jesus
Ayoyi game da Conspire against Jesus
Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,
Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.
Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,
To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu.