Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanitation

289 ayoyi · 10 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.

  2. Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku.

  3. Za ku iya cin kowane tsuntsu mai tsabta.

  4. Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,

  5. duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa,

  6. kowane irin hankaka,

  7. jimina, ƙururu, bubuƙuwa, kowane irin shaho,

  8. da mujiya, da babbar mujiya, ɗuskwi,

  9. kwasakwasa, ungulu, da babba da jaka,

  10. zalɓe, kowane irin jinjimi, katutu, da kuma jamage.

  11. Dukan ’yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe, haram ne a gare ku, kada ku ci su.

  12. Amma duk wata halitta mai fikafikai mai tsabta ce, za ku iya ci.

  13. Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa.

  14. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.

  15. Sai ku ci a cikin biranenku. Mutum marar tsabta da mai tsabta zai iya ci kamar yadda ake yi da barewa ko mariri.

  16. Amma kada fa ku ci jinin, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.

  17. In mutum ya yi laifin da ya isa kisa, aka kuwa rataye shi a itace,

  18. kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.

  19. In ɗaya daga cikin mazanku ya ƙazantu saboda zubar da maniyyi, sai yă fita daga sansani yă zauna waje da sansani.

  20. Amma yayinda yamma ke gabatowa sai yă wanke kansa, da fāɗuwar rana kuwa sai yă koma cikin sansani.

  21. Ku keɓe wuri waje da sansani inda za ku iya zuwa don yin bayan gari.

  22. Sai ku ɗauki wani abin tona ƙasa, sa’ad da kuka yi bayan gari, sai ku tona rami, ku rufe bayan garinku.

  23. Game da cututtukan kuturta, sai ku lura, ku yi yadda firistocin da suke Lawiyawa suka umarce ku. Dole ku lura ku bi abin da na umarce su.

  24. “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  25. “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”