Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sabbatic Year

45 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai,

  2. sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka.

  3. Sa’ad da kuka ’yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a kome da kuke yi.

  4. Sa’an nan Musa ya umarce su ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a shekara ta yafe basusuwa, a lokacin Bikin Tabanakul,

  5. sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.

  6. Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.

  7. ’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”

  8. Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.

  9. “Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi.

  10. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

  11. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce,

  12. ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’ Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba.

  13. Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.

  14. Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka ’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku.

  15. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.

  16. Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa.

  17. Shugabannin Yahuda da Urushalima, fadawa, firistoci da kuma dukan mutanen ƙasar waɗanda suka bi tsakanin ɗan maraƙin da aka yanka,

  18. zan ba da su ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namun jeji.

  19. “Zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da fadawansa ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, ga sojojin sarkin Babilon, waɗanda suke janye daga gare ku.

  20. Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.”