Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sabbatic Year

45 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba.

  2. “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.

  3. “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar,

  4. amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.

  5. Zan mai da ƙasarku kango har abokan gābanku da suke zama a wurin su yi mamaki.

  6. Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango.

  7. Sa’an nan ƙasar za tă ji daɗin hutun shekarun Asabbacinta, a dukan lokutan da take kango, ku kuwa kuna a ƙasar abokan gābanku, sa’an nan ƙasar za tă huta ta ji daɗin asabbatanta.

  8. A dukan lokutan da take kango, ƙasar za tă sami hutun da ba tă samu a lokutan asabbatan da kuke zama a cikinta ba.

  9. “ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu.

  10. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Ta haka ba za ku iya tsaya a gaban abokan gābanku ba.

  11. Za ku mutu a cikin al’ummai, ƙasar abokan gābanku za tă cinye ku.

  12. Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu.

  13. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,

  14. waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,

  15. A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi.

  16. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.

  17. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.

  18. Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo,

  19. in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau.

  20. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku.

  21. Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.

  22. In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi.

  23. Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi.

  24. Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku.

  25. Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuma ya fisshe ku. Shi ya sa nake ba ku wannan umarni a yau.