Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reed: Used as a measuring device of six cubits

15 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Used as a measuring device of six cubits

  1. A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa.

  2. Mutumin ya ce mini, “Ɗan mutum, duba da idanunka, ka ji da kunnuwanka ka kuma lura da kowane abin da zan nuna maka, gama abin da ya sa na kawo ka nan ke nan. Ka faɗa wa gidan Isra’ila duk abin da ka gani.”

  3. Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.

  4. Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne.

  5. Tsawon kowane ɗakin matsara kamu shida ne, fāɗinsa kuma kamu shida, kaurin bangayen da suka raba ɗaki da ɗaki kamu biyar ne. Zurfin madogarar ƙofar da yake dab da shirayin da yake fuskantar haikalin kamu shida ne.

  6. Sa’an nan ya auna shirayin hanyar shiga;

  7. Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida.

  8. Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar.

  9. Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.

  10. Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.

  11. Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya.

  12. “ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.

  13. Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can.

  14. Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa.

  15. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke.