Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reed: A water plant
Ayoyi game da A water plant
Wuriyoyi za su yi wari; rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe. Iwa da jema za su bushe,
haka ma tsire-tsire kusa da Nilu, a bakin kogi. Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.
Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.
An ƙwace mashigai aka ƙone fadamu da wuta, sojoji kuma suka giggice.”