Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Proverbs: Miscellany of

22 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Miscellany of

  1. Wani mutumin da yake zama a can ya ce, “Wane ne kuma mahaifinsu?” Ta haka sai wannan ya zama karin magana cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa?”

  2. Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.

  3. “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo?

  4. Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?

  5. Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama.

  6. Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ ”

  7. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!

  8. “A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce, “ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’

  9. “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra’ila mai cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’?

  10. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.’ Ka ce musu, ‘Kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

  11. “ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.”

  12. “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?

  13. “Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.

  14. Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.

  15. Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke. Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu in kuma sāka musu saboda ayyukansu.

  16. “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi.

  17. Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”

  18. Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.

  19. “Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa?

  20. Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”

  21. Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”

  22. Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.