Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Procrastination

64 ayoyi · 15 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.

  2. Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.

  3. Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”

  4. Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba?

  5. Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba?

  6. Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?

  7. Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

  8. Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga.

  9. Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba.

  10. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.

  11. Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.”

  12. Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.”

  13. Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya.

  14. Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”