Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Poor: Duty to

129 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Duty to

Tace bisa littafi
  1. “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

  2. In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana,

  3. domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.

  4. amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.

  5. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.

  6. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  7. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  8. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.

  9. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,

  10. sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  11. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.

  12. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.

  13. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.

  14. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.

  15. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.

  16. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.

  17. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.

  18. Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi.

  19. Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku.

  20. A ƙarshen kowace shekara uku, ku kawo dukan zakkarku na amfanin gona na wannan shekara, ku ajiye su a cikin birane,

  21. saboda Lawiyawa (waɗanda ba su da rabo ko gādo na kansu) da baƙo, da marayu, da kuma gwauraye, waɗanda suke zama a biranenku, su zo su ci su ƙoshi, ta haka Ubangiji Allahnku zai albarkace ku cikin dukan ayyukan hannuwanku.

  22. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.

  23. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.

  24. Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo,

  25. in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau.