Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Poor: Unclassified scriptures relating to

72 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.

  2. “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.

  3. “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.

  4. Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

  5. Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”

  6. Sa’an nan dukan mutane suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci, gama yanzu sun fahimci kalmomin da aka karanta musu.

  7. Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,

  8. domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.

  9. Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.

  10. Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu.

  11. Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo.

  12. Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?

  13. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  14. “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,

  15. in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,

  16. amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.

  17. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,

  18. kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,

  19. in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,

  20. bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.

  21. wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

  22. Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;

  23. Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

  24. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

  25. Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.