Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Oath: Attributed to God

21 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Attributed to God

  1. ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba,

  2. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,

  3. Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  4. alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.

  5. Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,

  6. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.

  7. Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.

  8. Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”

  9. Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ”

  10. Na rantse da kaina,” in ji Ubangiji, “cewa Bozra za tă zama kufai da kuma abin tsoro, abin dariya da abin la’ana; kuma dukan garuruwanta za su kasance kufai har abada.”

  11. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka.

  12. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

  13. Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  14. Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?

  15. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.

  16. Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,

  17. cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”

  18. Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa.

  19. shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”

  20. Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.

  21. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!