Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Oath

85 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba,

  2. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  3. “In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida,

  4. rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba.

  5. “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.

  6. “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,

  7. ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,

  8. sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.

  9. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  10. “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  11. Sa’an nan firist zai sa tă yi rantsuwa, yă kuma ce mata, “In ba wani mutumin da ya kwana da ke kuma ba ki kauce kin ƙazantar da kanki yayinda kike auren mijinki ba, kada wannan ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, yă cuce ki.

  12. Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,”

  13. (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura.

  14. Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.”

  15. “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.

  16. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.

  17. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.

  18. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa.

  19. Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.

  20. “Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan,

  21. sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa.

  22. Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

  23. Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

  24. wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,

  25. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,