Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Measures

41 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni?

  2. Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’

  3. Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa.

  4. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci.

  5. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba,

  6. A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa.

  7. Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu.

  8. Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda).

  9. Har yanzu zan manta, ya muguwar gida da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?

  10. In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.

  11. A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.

  12. Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.

  13. Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.

  14. Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in.

  15. Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.

  16. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke.