Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Measures

41 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45.

  2. Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.

  3. (Omer guda, daidai ne da kashi ɗaya bisa goma na Efa.)

  4. Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

  5. Zai zama murabba’i, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kuma kamu ɗaya, a naɗe shi biyu.

  6. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  7. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi.

  8. “A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai.

  9. Firist ɗin zai ɗiba daga moɗan mai ɗin ya zuba a tafin hannunsa na hagu,

  10. “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.

  11. (Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)

  12. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.

  13. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  14. Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara.

  15. Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

  16. Aka yi babban yunwa a cikin birnin. Saboda daɗewar wannan kewayewar da aka yi wa birnin, sai yunwa ta ɓarke a birnin, har ana sayar da kan jaki a kan shekel tamanin, kashin kurciya kuma a kan shekel biyar.

  17. Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.

  18. Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,

  19. Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.

  20. “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.

  21. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela

  22. Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.

  23. Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.

  24. Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”

  25. Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.