Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Master

39 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “In mutum ya dūke bawansa ko baiwarsa da sanda, sai bawan ko baiwar ta mutu saboda dūkan, dole a hukunta shi,

  2. amma ba za a hukunta shi ba, in bawan ko baiwar ta tashi, bayan kwana ɗaya ko biyu, tun da bawan ko baiwar mallakarsa ne.

  3. “In mutum ya bugi bawa ko baiwa a ido, har idon ya lalace, dole yă ’yantar da shi ko ita, maimakon ido.

  4. In kuma ya fangare haƙorin bawa ko baiwa, dole yă ’yantar da bawan ko baiwar, a maimakon haƙorin.

  5. “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.

  6. Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku.

  7. amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka.

  8. Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.

  9. Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.

  10. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,

  11. me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

  12. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  13. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

  14. In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.

  15. In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.

  16. “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu.

  17. “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  18. Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”

  19. Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub,me za su ce game da mutanen gidansa?

  20. “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.

  21. Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”

  22. Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”

  23. Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.

  24. Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.

  25. Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit.