Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Master

39 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake.

  2. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.

  3. To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa.

  4. Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.

  5. Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.

  6. Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.”

  7. Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.

  8. Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.

  9. Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.

  10. Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.

  11. Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.

  12. Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani

  13. ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.

  14. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.