Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Justification

132 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.

  2. Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”

  3. Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.

  4. Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu.

  5. Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.

  6. Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.

  7. Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.

  8. Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.

  9. Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi.

  10. Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi.

  11. In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau.

  12. Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne.

  13. Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.

  14. Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.

  15. To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.

  16. Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi.

  17. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;

  18. amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina.

  19. Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa?

  20. Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  21. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

  22. Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

  23. Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.

  24. Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.

  25. Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;