Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Inspiration: General references

20 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

  1. Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.

  2. Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

  3. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattaro mini dattawa saba’in daga cikin mutanen Isra’ila, waɗanda aka sani su ne dattawa da kuma shugabanni a cikin jama’a. Ka sa su zo Tentin Sujada, su tsaya a can tare da kai.

  4. Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.

  5. “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.

  6. Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba,

  7. amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ”

  8. Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’

  9. Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”

  10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”

  11. Saboda haka Musa ya fita ya gaya wa jama’a abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tattaro dattawansu saba’in, ya sa suka tsaya kewaye da Tentin Sujada.

  12. Sa’an nan Ubangiji ya sauko daga girgije, ya yi magana da shi, ya kuma ɗauke Ruhun da yake kan Musa ya ɗora shi a kan dattawa saba’in nan. Sa’ad da Ruhun ya zauna a kansu, sai suka yi annabci, amma daga wannan ba su ƙara yin haka kuma ba.

  13. To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin.

  14. Wani saurayi ya sheƙa a guje zuwa wajen Musa ya ce, “Eldad da Medad suna can suna annabci a sansani.”

  15. Sai Yoshuwa ɗan Nun, wanda yake mataimakin Musa tun yana saurayi, ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, Musa, ka hana su!”

  16. Amma Musa ya amsa ya ce, “Kana kishi domina ne? Da ma a ce dukan mutanen Ubangiji annabawa ne, da ma a kuma ce Ubangiji ya sa Ruhunsa a kansu mana!”

  17. “Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa,

  18. gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”

  19. A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho,

  20. wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”