Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ingratitude

62 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka.

  2. Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.

  3. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.

  4. Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.

  5. Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.

  6. “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.

  7. Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.

  8. “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”

  9. “Ya ku mutanena, me na yi muku? Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.

  10. Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.

  11. Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran?

  12. Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”