Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Decision

41 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma mutumin Allah ya amsa wa sarki, “Ko da za ka ba rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuwa zan ci abinci, ko in sha ruwa a can ba.

  2. Gama an umarce ni ta wurin kalmar Ubangiji, aka ce, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ”

  3. Saboda haka ya ɗauki wata hanya, bai kuwa koma ta hanyar da ya zo Betel ba.

  4. Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.

  5. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.

  6. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.

  7. Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”

  8. Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”

  9. Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”

  10. Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”

  11. Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”

  12. Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”

  13. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.

  14. “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.

  15. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki,

  16. ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  17. To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,

  18. ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.

  19. Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.

  20. Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.

  21. Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,

  22. ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,

  23. Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.

  24. Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.

  25. Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.