Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Chastity

60 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.

  2. Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace.

  3. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  4. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  5. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  6. Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu.

  7. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu.

  8. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.

  9. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.

  10. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.