Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Blasphemy

90 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya.

  2. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ”

  3. “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’

  4. “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki?

  5. Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.

  6. Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

  7. Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”

  8. Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

  9. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,

  10. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.

  11. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  12. Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu.

  13. Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”

  14. Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu.

  15. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama.