Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Blasphemy

90 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani.

  2. Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.)

  3. Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi.

  4. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  5. “Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu.

  6. Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa,

  7. duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.

  8. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  9. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  10. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

  11. wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.

  12. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.

  13. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

  14. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?

  15. Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?

  16. Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne

  17. da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?

  18. Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.

  19. Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?

  20. Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?

  21. In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?

  22. Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?

  23. Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.

  24. Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.

  25. domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,