Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Affections

39 ayoyi · 12 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.

  3. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  4. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

  5. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.

  6. Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.

  7. Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.

  8. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

  9. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.

  10. “Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa. Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho. Ku furta wa mutanena tawayensu da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu.

  11. Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.

  12. Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba.

  13. Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.

  14. “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;

  15. Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,

  16. Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’

  17. Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.

  18. “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.

  19. Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”

  20. su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi.

  21. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi

  22. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.

  23. A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  24. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  25. Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.