Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Adultery

242 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma in kin kauce yayinda kike auren mijinki, kika kuma ƙazantar da kanki ta wurin kwana da wani dabam da ba mijinki ba,”

  2. (a nan firist zai sa macen a ƙarƙashin la’anar rantsuwa cewa) “bari Ubangiji yă sa mutanenki su la’ance ki, su kuma yi Allah wadai da ke, sa’ad da Ubangiji ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbura.

  3. Bari wannan ruwa mai jawo la’ana, yă shiga jikinki saboda cikinki yă kumbura, cinyarki kuma yă shanye.” “ ‘Sai macen tă ce, “Amin. Bari yă zama haka.”

  4. “ ‘Firist zai rubuta waɗannan la’anoni a littafi, sa’an nan yă wanke su cikin ruwa mai ɗaci.

  5. Sai yă sa macen tă sha ruwa mai ɗaci, mai jawo la’ana, wannan ruwa kuwa zai shiga cikinta yă kawo mata wahala mai zafi.

  6. Firist zai karɓi hadaya ta gari don kishi daga hannuwanta, yă kaɗa shi a gaban Ubangiji sa’an nan yă kawo a bagade.

  7. Sa’an nan firist zai ɗiba hatsi na hadaya cike da hannunsa don hadayar tunawa, yă kuma ƙone a bagade; bayan haka sai yă sa macen tă sha ruwan.

  8. In ta ƙazantar da kanta ta kuma ci amanar mijinta, to, yayinda aka sa tă sha ruwa mai jawo la’ana, ruwan zai shiga cikinta, yă jawo mata wahala mai zafi; cikinta zai kumbura, cinyarta kuma yă shanye, tă kuwa zama la’ananniya a cikin mutanenta.

  9. Amma fa, in macen ba tă ƙazantar da kanta ba, ba tă kuma da ƙazanta, za a kuɓutar da ita daga laifin, za tă kuma iya haihuwa.

  10. “ ‘Wannan dai, ita ce dokar kishi sa’ad da mace ta kauce, ta kuma ƙazantar da kanta yayinda take aure da mijinta,

  11. ko kuma sa’ad da mijin yana kishi domin yana shakkar matarsa. Firist zai sa tă tsaya a gaban Ubangiji, yă kuma yi amfani da wannan doka gaba ɗaya a kanta.

  12. Kada ka yi zina.

  13. In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta

  14. ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, “Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce,”

  15. sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin.

  16. Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.

  17. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,

  18. dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.

  19. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.

  20. Amma fa in zarge gaskiya ne, ba a kuwa sami shaidar budurcin yarinyar ba,

  21. sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  22. In aka kama wani yana kwance da matar wani, dole a kashe dukansu biyu, wato, mutumin da ya kwana da matar da kuma matar. Dole a fid da mugu daga Isra’ila.

  23. In mutum ya sadu da budurwa a gari wadda aka yi alkawarin aure, ya kuma kwana da ita

  24. sai ku ɗauki su biyu zuwa ƙofar wannan gari, ku jajjefe su da dutse har su mutum, za a kashe yarinyar domin tana a cikin gari ba ta kuwa yi ihu neman taimako ba, za a kashe mutumin domin ya yi lalata da matar wani. Dole ku fi da mugu daga cikinku.

  25. Amma in a bayan gari ne mutumin ya sadu da yarinyar da aka yi alkawari aure, ya kuma yi mata fyaɗe, mutumin da ya yi wannan ne kaɗai zai mutu.