circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Luka 18:32kusan 33 M.
Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau,
- Luka 18:33kusan 33 M.
za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”
- Luka 18:34kusan 33 M.
Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.
- Luka 18:35kusan 33 M.
Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara.
- Luka 18:36kusan 33 M.
Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa.
- Luka 18:37kusan 33 M.
Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”
- Luka 18:38kusan 33 M.
Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
- Luka 18:39kusan 33 M.
Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
- Luka 18:40kusan 33 M.
Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce,
- Luka 18:41kusan 33 M.
“Me kake so in yi maka?” Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”
- Luka 18:42kusan 33 M.
Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.”
- Luka 18:43kusan 33 M.
Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.
- Luka 19:1kusan 33 M.
Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta.
- Luka 19:2kusan 33 M.
Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma.
- Luka 19:3kusan 33 M.
Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne.
- Luka 19:4kusan 33 M.
Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.
- Luka 19:5kusan 33 M.
Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”
- Luka 19:6kusan 33 M.
Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.
- Luka 19:7kusan 33 M.
Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”
- Luka 19:8kusan 33 M.
Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
- Luka 19:9kusan 33 M.
Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.
- Luka 19:10kusan 33 M.
Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
- Luka 19:11kusan 33 M.
Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan.
- Luka 19:12kusan 33 M.
Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo.
- Luka 19:13kusan 33 M.
Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’